Amirka ta zargi China da yaudara kan Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 29.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta zargi China da yaudara kan Koriya ta Arewa

A cewar kafar yada labaran Chosun Ilbo a Koriya ta Kudu an dauki hotuna na tauraron dan Adam wanda ya gano jiragen dakon mai na China na kai mai a Koriya ta Arewa.

Shugaba Donald Trump na Amirka da a lokuta da dama ke yaba wa kasar China kan matsin lamba da take yi ga Koriya ta Arewa, a ranar Alhamis din jiya ya ce, kasar ta China a kokarin da ake yi na gigita mahukuntan na birnin Pyongyang ta hanyar hana masu samun albarkatun mai, na yin zagon kasa ga wannan shiri da ake ganin zai kai ga kwantar da rikicin da ake da kasar ta Koriya ta Arewa ta hanyar laluma.

Da yake wallafa jawabinsa ta hanyar shafin Twitter kamar yadda ya saba, Shugaba Trump ya ce ya ji takaici yadda aka ga China na tura mai zuwa kasar ta Koriya ta Arewa. Ya ce muddin hakan ya ci gaba da faruwa ba za a wanye da Koriya ta Arewa ta hanyar laluma ba.

A wani rahoto da kafar yada labaran Chosun Ilbo, na Koriya ta Kudu ta wallafa ta ce wata majiya daga mahukuntan birnin Seoul a farkon wannan wata ta ba shi tabbacin cewa akwai hotunan tauraron dan Adam da aka tabbatar da cewa sun dauko hoton jiragen ruwa mallakar kasar China dauke da dakon mai na isa Koriya ta Arewa.