1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yaba matakan tsaro da ke a Abuja

October 29, 2022

Bayan wani gargadi kan yiwuwar samun hare-hare a Najeriya da Afirka ta Kudu, gwamnatin Amirka ta yaba wa kasashen biyu kan abin da ta ce ingantuwar yanayi na tsaron.

https://p.dw.com/p/4IpJc
Shugaba Joe Biden na kasar Amirka
Hoto: Jim LoScalzo/ZUMA Wire/IMAGO

Amirka ta yaba da kokarin da kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu ke yi a kan tsaro, bayan wani kashedin da ta yi na yiwuwar afka wa Abuja fadar gwamnatin Najeriya da hare-haren ta'addanci da ma wasu wurare da ke wajen birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai Amirkar ta yi kiran ma'aikatan jakadancinta da ke Abuja da su fice daga Najeriya, kwana guda bayan ta yi hakan ga su ma 'ya'yanta da ke a Afirka ta Kudu.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, ya nuna rashin jin dadi ganin yadda Amirkar ta yi gaban kanta wajen bayyana hadarin ba tare da ta tuntubi gwamnatin kasar ba.

Sai dai kuma ma'aikatar kula da hakokin kasashen wajen Amirka, ta yaba wa kokarin da Najeriya da Afirka ta Kudun ke yi a bangaren tsaurara tsaro da nufin tinkarar duk wani hari da ya doshi manyan birnanen kasashen biyu da Amirkar ta ce ta hango.