Amirka ta janye tallafinta ga sake gina Siriya | Labarai | DW | 17.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta janye tallafinta ga sake gina Siriya

Kasar Amirka ta sanar da dakatar da tallafin kudi miliyan 230 na Dalar Amirka da ta yi alkawarin zubawa a shirin sake gina kasar Siriya.

Heather Nauert mataimakiyar sakataren harakokin waje kana kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Amirka ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Juma'a inda ta ce Amirka ta dauki matakin karkata akalar wadannan kudade zuwa wasu bukatun na daban ta la'akari da yadda kasashen duniya da dama suka shigo cikin shirin sake gina kasar ta Siriya. 

Ko a wannan Juma'ar dai kasar Saudiyya ta sanar da bayar da gudunmawar miliyan 100 na Dalar Amirka ga shirin sake gina yankin Arewa maso gabashin kasar ta Siriya wanda ya kasance a karkashin ikon Kungiyar IS a shekarun baya. Ita ma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi alkawarin tallafa wa shirin da kudi Dala miliyan 50.