1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta bukaci daukar sabbin matakai kan Koriya ta Arewa

Gazali Abdou Tasawa
September 5, 2017

Amirka da wasu kasashe kawayenta sun bayyana bukatar saka wa Koriya ta Arewa takunkumi mafi tsanani bayan gwaji na shida na makami mai lizzami da ta yi. 

https://p.dw.com/p/2jM5G
USA UN-Sicherheitsrat in New York - US-Botschafterin Nikki Haley
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Matthews

Amirka da wasu kasashe kawayenta sun bayyana bukatar saka wa Koriya ta Arewa takunkumi mafi tsanani idan ana son taka wa shirinta na nukila birki ta hanyar diplomasiyya bayan gwaji na shida na makami mai lizzami da ta yi. 

Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ce ta bayyana wannan bukata a lokacin wani taron gaggawa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira a jiya Litinin inda ta ce a bayyane ta ke cewa a yau Koriya ta Arewa ba abin da take bukata illa yaki.

"Take-taken Kim Jong Un ba batu ba ne na neman kare kasarsa ba. Wuce gona da irin da yake yi wajen gwaje gwajen makamai masu lizzami da barazanar nukiliyar da ya ke yi na nuni karara da cewa yana bukatar yaki ne kawai"

To sai dai kasashen Rasha da Chaina kawayen Koriya ta Arewar sun bayyana rashin amincewarsu da duk wani sabon mataki na amfani da karfi da Amirkar da kawayen nata ke son dauka kan Koriya ta Arewar suna masu cewa tsaurara matakai kan wannan kasa ba shi ne zai taimaka ga shawon kan rikicin ba.