Amirka da Jamus sun soki harin Aleppo | Labarai | DW | 30.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Jamus sun soki harin Aleppo

Yayin da Rasha da Siriya ke ci gaba da luguden wuta a Siriya, shugabannin Amirka da Jamus sun baiyana matukar damuwa.

Shugaban Amirka Barack Obama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun yi kakkausar suka a kan abin da suka kira ta'asar hare hare ta sama da sojojin Rasha da na Siriya suke yi a gabashin birnin Aleppo.  

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Amirka ta ce shugabannin biyu sun kuma ce gwamnatocin Rasha da Siriya su na da babban nauyi a wuyansu na tabbatar da kawo karshen fadan da kuma bada damar kai kayan agaji ga jama'a a yankunan da aka yiwa kawanya. Merkel ta Obama sun tattauna ne ta wayar Tarho a cewar sanarwar. 

A waje guda kuma babban jami'in taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Stephen O'Brien ya sanya ayar tambaya cewa anya ta'asa da kasashe kashen da ake yi a Syria basu isa su ja hankalin al'ummar duniya su takawa lamarin birki ba?

"Yace wannan wata jarrabawa ce muhimmiya ta karfin tasiri da kudirin shugabanni su tashi tsayin daka su dauki mataki bisa daftarin Majalisar Dinkin Duniya su kare jama'ar Siriya daga wannan mummunan yaki."