Amirka ba ta buƙatar a ɗaga zaɓen Najeriya | Labarai | DW | 07.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ba ta buƙatar a ɗaga zaɓen Najeriya

Fadar gwamnatin Amirka, ta yi kira da a gudanar da zaɓen Najeriya a ranar da aka tsaida ta 14 ga wannan wata tare da fatan ganin an yi shi cikin kwaciyar hankali.

Ƙasar Amirka ta yi kira da a gudanar da zaɓuɓɓukan ƙasar Najeriya a ranar da aka tsaida ta 14 ga wata, yayin da a wannan Asabar ɗin ce (07.02.2015) hukumar zaɓen ƙasar INEC za ta fitar da sakamako na ƙarshe kan ko za'a ɗage zaɓen ko akasin haka. Da take magana yayin wata sanarwa kakakin fadar gwamnatin ƙasar ta Amirka Marie Harf, ta sanar cewar, Amirka na fatan ganin an yi wannan zaɓe cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata ƙulla-ƙulla ba, inda ta yi kira ga 'yan takarar baki ɗaya da ma sauran al'ummar ƙasar ta Najeriya da su yi watsi da duk wani yanayi da zai iya kawo tashin hankali a wannan ƙasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane