Amfani da rediyon wajen taimakon jama′a | Himma dai Matasa | DW | 16.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Amfani da rediyon wajen taimakon jama'a

Wata 'yar gwagwarmaya ta kafa gidan rediyo domin taimakon al'umma a Jamhuriyar Nijar da ke yankin yammacin Afirka.

Wata mai kishin kasa a Janhuriyar Nijar ta kafa gidan rediyo domin taimakon al'ummar yankinta. Ita dai wannan 'yar kishin kasa mai suna Chatou Mahmadou mamba ce a wata kungiya mai zaman kanta mai suna "Espace Citoyen" a harshen Faransanci kuma mai kare hakkin dan Adam ta kafa gidan rediyon ne domin bai wa al'ummar ciki da wajen birnin Yamai damar tofa albarkacin bakinsu game da abin da ke ci masu tuwo a kwarya.

Chatou ta kumayi amfani da gidan radiyon domin yada wasu manufofi na Al,umma da ke bukatar canji, hakanne yasa ta rika tursasawa hukumomi sauke wasu nauye nauye da suka rataya a wuyansu na Al,umma:

An rushe wurare a wata unguwa cikin birnin Yamai a janhuriyar ta Nijar inda aka rushe wasu gidaje da dama, aka gina wata sabuwar gada da kuma wasu hanyoyi. Yawancin mazauna yankunan sun yi asarar gidajensu hakan ne ya sa Chatou ta tsaya tsayin daka taba mazauna ungawar damar kai korafinsu ga hukumomin da suka dace, ta ce ta hakan ana samun nasara sosai:

"Idan muka gabatar da shiri kamar wannan, masu madafun iko sukan yi kokarin kamanta kyakkyawan shugabanci. Kuma sukan kaurace wa yin ba dai dai ba ga al'umma saboda idanummu na kansu, kuma na fahimci cewa hakan yana canzawa mahukunta dabi'u, kuma tabbas idan akwai mutane masu zimma to abubuwa za su canza"

Gundarin Manufar kafa wannan gidan radiyo shi ne dan mata da matasa, kuma suna gabatar da shirye shiryensu a birnin Yamai dama wasu yankuna, kuma sanannen gidan radiyo ne wajen fadakarwa da wayar da kan al'umma ya kafa wata kungiya ta matasa mai mambobi 350 wadanda ke yada manufarsu dangane da yancin dan Adam da kuma sha'ani da ya shafi siyasa.

Har ila yau gidan radiyan yakan tabo batutuwa da suka shafi 'yancin dan Adam da yanayin yaruwar mata da gurbataccewar ilmi a janhuriyar Nijar da kuma sha'anin cin hanci.

Chatou ta ce gwamnati tana kallon shirye-shiryen a matsayin suka gareta amma duk da haka manema labarai na samun walwala.

Chatou Mahmadou mai shekaru arba'in da daya da haihuwa ta girma ne a wani yanki na birnin Yamai, kuma ta koyi jarintar fuskantar kalubale ne tun daga gidansu. Iyayenta sun bata damar zabar fannin da take so wajen gudanar da rayuwarta, wanda hakan ne ya karfafa mata gwiwar taimaka wa al'umma, kamar yadda mahaifiyar ta Fati Mahmadou ta bayyana

"Tun tana karama ta kasance mai hazaka, wadda a koda yaushe ke san binciken abunda ke faruwa a yankinta dama wasu wurare. Tana yawan tambayar abubuwa mu kuma mukan bata amsa duk da ba komai muka sani ba"

Jarumta dai da kwarin gwiwa suka sa Chatou take fita tana haduwa da mutane iri daban-daban, musamma a wasu lokutan marasa galihu.

Sauti da bidiyo akan labarin