1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun sulhu tsakanin yan jam'iyar PDP

September 16, 2013

Ɓangarorin sabuwa da na tsohuwar PDP sun buɗe babin sulhu da nufin kawo karshen banbancin da ke barazana ga tasirin jamiyyar.

https://p.dw.com/p/19iLy
Jigawa State Governor Sule Lamido, speaks on September 27, 2010 in Dutse about the flood disaster in Nigeria's north. Officials in Jigawa state say two dams opened last month caused flooding that displaced some two million people. They have heavily criticised the agency in charge of the barriers, alleging similar episodes have occurred in the past. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Sule LamidoHoto: Getty Images

An dai kai nuna yatsa, dama kokari na baiwa hammata iska a kokarin kaiwa ga hujewar lemar jamiyyar PDP da marka marka. To sai dai kuma yanzu haka an kai ga sayen basilla a tsakanin banagren shugaba Jonathan na jamiyyar PDP da kuma yan uwansa gwamnoni bakwai dake tawaye da nufin kaiwa ga kokarin dinkin lemar da tai nisa a cikin zub da ruwa sannan kuma ke barazana ga abincin kowa.

Bangarorin biyu dai sun kamalla wani taron su cikin ranar Litinin tare da yanke hukuncin tsagaita wuta da kila samar da sabuwar damar sulhun dake da tasiri ga makomar PDP mai mulkin. Rikici a tsakanin sabuwa da tsohuwar PDP dai na nufin rage karfi dama kila barazanar tazo karshe a cikin babakeren jamiyyar dake da shirin mulkar kasar har na tsawon wasu shekaru 60.

To sai dai kuma duk da cewar sun kai ga bayyana ga hotunan television da nufin nuna alamar tare, babu dai wani sharadin da ya fito a bakin koda guda daga cikin mahalarta taron da ke cike da jerin sharudan neman sake tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jamiyyar. Abun kuma da a cewar Dr. Umar Ardo dake zaman masanin harkokin siyasar kasar ke nuna alamun ayar taambaya cikin kalaman nasu da kuma ragowar kaya da tsidau din dake cikin tafiyar tabbatar da sulhun nasu.

Nigeria Plakat Präsident Goodluck Jonathan Archiv 2011
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Kokarin zama gidan jiya ko kuma bude sabon nau'in tattaunawa dai daga dukkan alamu karatun na shugaba jonathan dama yan uwansa yan tawayen dai na nuna karatu na tanatsu a bangaren yan PDP da a baya ke da al'adar kisa da shan romo akushi guda. Sannu a hankali dai rikicn dake bazuwa ya zuwa jihohi daban daban na jamiyyar dai na neman cin karfin PDP da ke fuskantar adawa mafi girma a kasar dama kila fagen siyasar da siyasar duniya ta kai ga sauyin fasalinsa a yanzu haka.

Abun kuma da ya jefa daukacin bangarorin biyu tsaka mai wuyar mantawa da nasu banbance banbancen ko kuma asarar damar rawar gaban hantsi cikin harkokin siyasar kasar mai kara duhu da ramuka. Duk da cewar dai sai a watan gobe na October ne dai aka tsara bangarorin zasu dora kan karatun nasu dai can a cikin Legacy House dake zaman offishi ga shugaban jam'iyyar dai murna har kunne tsakanin mabiya dake kallon rikicikn a matsayin barazana cikin garinsu. Senator Saidu Umar Kumo dai na zaman mashawarcin Bamangan bisa harkoki na siyasa, kuma a cewar sa lale kuma marhabin da kokri na tsagaita wutar.

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba da zai kunshi irin sabbabin ministocin da shugaban yake shirin ya nada da kuma irin rawar da suke shirin takawa a cikin rassan jamiyyar na jihohin nasu. Tuni dai ake hasashen yiwuwar nadin masu adawa da gwamnonin da nufin haifar da kishiya dama kila takun birki cikin harkokin gwamanonin bakwai a jihohinsu.

CORRECTION REMOVES REFERENCE
Daya daga cikin yan tawayen jam'iyar PDP gwamnatin jihar Rivers Rotimi Chibuike AmaechiHoto: picture alliance/AP Photo

.Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu