1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIngila

Ko Al-Sharaa ya fita daga al Qaeda da IS?

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 7, 2025

Birtaniya ta sanar da cewa, ta janyewa sabon shugaban rikon kwarya na Siriya Ahmad al-Sharaa takunkumin da ta kakaba masa.

https://p.dw.com/p/53HDk
Siriya | Shugaban Kasa | Ahmed al-Sharaa | Takunkumi | Birtaniya
Shugaban kasar Siriya Ahmed al-SharaaHoto: Syrian Presidency/AFP

Birtaniyan ta kuma sanar a shafinta na Internet cewa, za ta cirewa ministan cikin gida na Siriyan Anas Khattab takunkumi. Duka mutanen biyu dai, sun fuskanci takunkumin karya tattalin arziki da ke da nasaba da kungiyoyin 'yan ta'addan IS da  al Qaeda.

Wannan na zuwa ne bayan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya janye nasa takunkumin da ya kakabawa shugaban na Siriya, gabanin ganawar Shugaba Ahmad al-Sharaa da takwaransa na Amurka Donald Trump a mako mai zuwa.

Shugaba al-Sharaa da a baya aka sani da Abu Mohammad al-Julani ya zamo shugaban Siriya ne a watan Janairu, bayan kifar da gwamnatin kama-karyar kasar ta Bashar al-Assad a watan Disambar bara karkashin jagorancin kungiyarsa ta Hayat Tahrir al-Sham wato HTS.