Al-ka'ida ta sako dan Faransa bayan shekaru uku
December 9, 2014Wannan mutumin dan asalin kasar Faransa ya samu kansa a yau Talata ne bayan da Kungiyar Alka'ida reshen arewacin Afrika ta yi garkuwa da shi fiye da tsawon shekaru uku.
Serge Lazarevic ya samu kansa ne bayan wata tattaunawa tsakanin mahukuntan Faransa da Mali da Jamhuriyar Nijar, a cewar shugaban Fransa yana cikin koshin lafiya duk kuwa da cewa yana hannune na masu garkuwa da mutane.
Sakin nasa dai na zuwa ne kwanaki bayan da aka sako wasu da aka kame saboda wasu batutuwa masu alaka da garkuwar da shi daga gidan kaso.
Bayyanar labarin sakin na Lazarevic dai ya sanya farinciki a zukatan 'yan uwansa dama al'ummar kasar ta Faransa ciki kuwa har da wadanda a baya suma aka yi garkuwa da su ganin yadda a karshen makon da ya gabata wani yunkurin sojan Amirka ya gaza kwato wani dan Amirka da Afrika ta Kudu da reshen Alka'ida a Yemen ya yi garkuwa da su.