Al-Ka′ida ta dauki alhakin harin Charlie Hebdo | Labarai | DW | 14.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Ka'ida ta dauki alhakin harin Charlie Hebdo

Kungiyar Al-Ka'ida reshen Yemen ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari a gidan mujallar barkwancin nan ta Charlie Hebdo wacce ke fita a mako-mako.

Al-Kaida in Jemen übernimmt Verantwortung für die Anschläge in Paris 14.01.2015

Nasser al-Ansi daya daga cikin shugabannin Al-Ka'ida a Yemen

Kungiyar ta Al-Ka'ida ta ce wannan wani bangare ne na irin ramuwar gayya kan gidan mujallar saboda zanen da take fitarwa na barkwancin wai da sunan fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Cikin wani faifayen bidiyo da ta fitar, wani da ake kira Nasser al-Ansi da ke zama daya daga cikin shugabannin wannan kungiyar Al-Ka'ida a reshen na Yemen, ya bayyana cewa sun tura a aiwatar da wannan aiki ne saboda kalaman batanci da mujallar kan fitar.

Ansi ya ce wannan kuma na zama cika umarni na shugabansu Ayman Zawahiri.

Ita dai wannan kungiya da ke a mashigar tekun Arebiya da aka girka a watan Janairu na shekarar 2009, ta kasance reshen kungiyar ta Al-Ka'ida da ke a Yemen da kasar Saudiyya, wacce kuma mahukuntan birnin Washington ke bayyana ta a matsayin wata kungiya ta masu jihadi da ke zama barazana ga duniya, dan haka ta kaddamar da yaki kan kungiyar da shugabanninta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal