Akinwumi Adesina ya gana da Buhari | Siyasa | DW | 27.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Akinwumi Adesina ya gana da Buhari

Shugaban bankin raya kasashen Afirka ADB ya tattauna da shugaban Najeriya domin tallafa wa kasar da kudaden bashi miliyan dubu daya domin aiwatar da kasafin kudin kasar na bana.

Bayan kammala wata ganawarsa da jami'an gwamnatin kasar dai shugaban bankin Akinwumi Adesina ya ce bankin ya dau aniyar taka rawa wajen taimaka wa kasar fitowa daga matsin da take ciki  a halin yanzu. Ko bayan nan dai Adesina da ke ziyarar aikinsa ta farko cikin kasar tun bayan kama aiki a shekarar bara dai ya ce kasar ta Najeriya da ke zaman mafi jari a cikin bankin na da mahimmancin gaske ga banki.

Shugaban bankin raya kasashen Afirka ADB Akinwumi Adesina

Shugaban bankin raya kasashen Afirka ADB Akinwumi Adesina


.
Ko bayan bashin kasafin dai har ila yau kuma bankin ADB ya ce yana shirin kashe tsabar kudi har dalar Amirka miliyan dubu hudu da dari daya a tsakanin shekarar bana zuwa ta badi  a matsayin bashin da ya ce zai bai wa kasar domin habbaka harkokin noma da wuta da kuma hako ma'adinai na karkashin kasa.Hukumar gudanarwa ta bankin za ta zauna ta yi nazarin wani bashin dalar Amirka miliyan dubu daya ,ko bayan nan dai kuma akwai wasu kalubalen da tattalin arzikin ke fuskanta a kokarinsa na karin karfi bankin zai ba da bashin da ya kai dalar Amirka miliyan dubu hudu da dari daya a tsakanin shekara ta 2016 da kuma da 2017 domin zuba jari a cikin harkoki na wuta da bashin noma da kuma kananan masana'antu.

Sauti da bidiyo akan labarin