1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aiyukan sabuwar gwamnati sun kankama a Najeriya

Pinado Abdu WabaJune 4, 2015

Kamar yadda sabon shugaba Buhari ya bayyana a jawabinsa na farko, yaki da Boko Haram ne kan gaba a ajandarsa domin tabbatarwa al'ummar yankin da ta addaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/1Fbiw
Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Ranar 29 ga watan Mayu aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa na 16 a Najeriya. Babban kalubalen da ke fiskantar sabuwar gwamnatin ita ce tsaro, sannan cin hanci da rashawa da rashin aikin yi. Tuni dai shugaban ya gana da shugabannin Nijar da Chadi wadanda tun baya suke taimakawa wajen yaki da kungiyar Boko Haram wadda ke faman nakasa yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Ga dai wasu daga cikin rahotannin da muka yi muku tanadi dangane da rantsuwar kama aikin na sa da ma irin hare-haren da Boko Haram ke kaiwa: