Aikin ceton jama′a a Nepal | Labarai | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin ceton jama'a a Nepal

Wata sabuwar girgizar ƙasar da ta auku a Nepal ta kashe mutane kusan 65.

Sojoji a ƙasar Nepal na ci gaba da neman mutanen da suka maƙale a cikin tarkaccen gine-ginen da suka ruguje. A sakamakon wata sabuwar girgizar ƙasar da ta auku a gabashin birnin Katmandu a lardin Dolakha a jiya Talata.

Gwamnatin ta ce ya zuwa yanzu mutane 65 girgiza wacce ke da ƙarfin maki bakwai da ɗigo ukku a mau'nin Richter ta rutsa da su yayin da wasu da dama suka jikata.