African Development Bank (AfDB) banki ne na raya kasashen Afirka da ke da cibiyarsa a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.
Daga cikin irin baubuwan da bankin ke yi sun hada da tabbatar da ci gaban Afirka da bunkasa tattalin arziki da kawar da matsalar dumamar yanayi da kuma samar da daidaito, gami da batun bunkasa makamashi.