1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Afrika na iya zama mai fada a ji a fannin makamashi

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 12, 2024

Shugaban Bankin bunkasa kasashen (AfDB) Dr Akinwumi Adesina ya nunar da cewa, ba da jimawa ba Afirka za ta zamo mai fada aji a fannin makamashin da ake sabuntawa.

https://p.dw.com/p/4dQu1
Afrika ist durch den Klimawandel völlig verzweifelt": AfDB-Präsident
Hoto: DW

Adesina ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar DW kan halin da Afirkan ke ciki na matsin tattalin arziki da sauyin yanayi. 

Yayin wannan tattaunawa da tashar DW, Shugaban bankin bunkasa kasashen Afirka Dr Akinwumi Adesina ya yi karin haske kan irin yadda al'amura ke tafiya a Afirka, yana mai bayyana yadda Afirka ke fama da matalar hauhawar farashi da kuma karuwar basussukan da ake bin kasashen nahiyar baya ga matsalar dumamar yanayi. Sai dai duk da haka Adesina ya nunar da yadda Afirka ke bunkasa cikin hanzari, a cewarsa 11 cikin kasashe 20 da tattalin arzikinsu ke bunkasa suna nahiyar duk da cewa har yanzu akwai burbushin matsalolin da annobar corona ta haifar a nahiyar da ma sauran matsaloli. 

Tsibirin Annobon a kasar Equatorial Guinea a Afirka
Hoto: Michael Runkel/robertharding/picture alliance

"A yanzu Afirka na yin asarar tsakanin dalar Amurka biliyan bakwai zuwa 15 a shekara sakamakon sauyin yanayi, bankinmu na bunkasa Afirka ya dauki matakin tabbatar da ganin sun samu daukin da ake bukata. Muna da shirye-shirye da muke gudanarwa kamar African Disaster Risk Insurance Facility, wanda ya taimaka gaya a Malawi ta hanyar tallafa wa miliyoyin manoma da fari ya cimmasu. Haka abin yake ga manoman Madagascar da Jamhuriyar Nijar da ma wasau kasashen da dama." 

Duk da yadda ake fama da cin hanci a kasashen Afirka da dama Adesina ya nunar da cewa Afirka na da makoma mai kyau kan batun sabunta makamashi, idan aka yi la'akari da yadda ake samun sama da kaso 60 cikin 100 na hasken rana a duniya a Afirkan da kuma filin noma kimanin kaso 65 cikin 100. A cewarsa hakan ya sanya nan gaba Afirka ka iya zama ja gaba a fannin makamashin da ake sabuntawa da kuma samar da abinci a duniya. wannan ne ma ya sanya bankin na bunkasa Afirka ke jin dadin yin kira ga masu zuba jari zuwa nahiyar, koda yake tilas kuma a jajirce wajen inganta abubuwa a nahiyar a cikin gida.

Dr Akinwumi Adesina a tsakiya yayin gabatar da rahoto kan cigaban Africa a Addis Ababa
Hoto: Tolani Alli/AfDB Group

"Ina ganin idan har muka kyautata yadda ake tafiyar da kudin al'umma tare da tabbatar da kula da albarkatun kasar da muke da su, muka kuma saka musu farashin da ya dace da tabbatar da cewa duk wanda ya kamata ya biya haraji yana biya za mu iya samar da abubuwa da dama."

Shugaban bankin bunkasa kasashen Afirka AfDB Dr Akinwumi Adesina ya kara da cewa akwai bukatar samar da gagarumin gyara a fannin aikin gona domin tabbatar da ganin kasashen Afirka suna iya ciyar da kansu, tabbas idan kuwa ba haka ba za a ci gaba da fuskantar matsaloli masu tarin yawa.