1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adesina ya sake zama shugaban bakin AFDB

Binta Aliyu Zurmi
August 27, 2020

An sake zaban shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwumi Adesina a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar bankin a wani wa'adi na biyu mai tsawon shekaru biyar.

https://p.dw.com/p/3hbeE
Akinwumi Adesina Porträt Entwicklungsbank Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Nedegeya

Adesina mai shekaru 60 da ke zama tsohon ministan noma a tarayyar Najeriya ya sami kaso dari cikin dari na kuri'un da aka jefa daga dukkanin bankunan mambobin yanki da ma wadanda ba na yankin ba. 

A shekarar 2015 ce Adesina ya zama dan Najeriya na farko da ya fara rike shugabancin wannan bankin da ke zama na biyar a jerin manyan cibiyoyin kudi na duniya masu ba da bashi. 

Sabon wa'adin zai fara ne daya ga watan Satumba.