1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manoma za su samu rancen dala miliyan 210

Abdul-raheem Hassan
December 14, 2021

Bankin raya kasashen Afirka za ta ba wa kananan manoman Najeriya tallafin rancen kudade dala miliyan 210 da zimmar bunkasa ayyukan noma da harkokin kiwo a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/44G2G
Nigeria Landwirtschaft Bauern
Hoto: Fati Abubakar/AFP

Wannan shi ne shi ne tallafi na farko karkashin wani shiri na musamman da bankin raya kasashen Afirka ta bullo da shi don rage wa manoma tsadar kaya. Shirin zai fara ne da jihohi bakwai na Najeriya, sannan daga baya za a fadada shirin zuwa wasu kasashen Afirka guda bakwai.

A yayin taron zuba jari a kasar Saudiyya a watan Oktoba na shekarar 2021, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Afirka ce ta fi ko ina yawan kasar yin noma. Sauran abokan hulda kamar Bankin Raya kasashen Musulunci da kuma asusun bunkasa noma na kasa da kasa, za su hada hannu wajen tallafawa aikin.

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya na da yawan gonaki sai dai kasar  na dogaro ne da shigo da kaya daga waje don ciyar da al'umarta fiye da mutane.