1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal AMA
November 27, 2020

Batun yakin neman zabe a Yuganda da dakatar da shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad daga aiki da yadda rikicin yankin Tigray ke kara kamari a Habasha sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3lvRX
Äthiopien Tigray Soldaten Kämpfer
Mayakan 'yan tawayen TigrayHoto: Eduardo Soteras/AFP/Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Habasha wato Ethiopia ta ce Tarayyar Afirka na son ta jagoranci tattaunawar kawo karshen rikicin yankin Tigray, yayin da al’umar yankin suka yi fatali da wa’adin da gwamnatin birnin Addis Ababa ta ba su. Jaridar ta ce jami’an diplomasiyyar Afirka na neman wata damar shiga tsakanin masu rikicin a Habasha domin kaucewa daga barazanar yin mummunan gumurzu a birnin Mekelle hedkwatar yankin Tigray, inda gwamnatin tsakiya da gwamnatin yankin ke fada da juna. A ranar Lahadi da yamma Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya ba wa kungiyar kwatar ‘yancin Tigray wato TPLF wa’adin sa’o’i 72 su ajiye makamansu ko kuma a dauki matakin a yi ta ta kare kansu.

Karin Bayani: Murkushe 'yan aware da karfin tuwo a Habasha

Äthiopien Amhara-Soldaten auf dem Weg nach Tigray
Mayakan Tigray dauke da makamaiHoto: Tiksa Negeri/REUTERS

Sai dai mayakan na kungiyar TPLF sun yi fatali da wa’adin. A daidai lokacin da kungiyar tarayyar Afirka ta fara yunkurin yin sulhu, inda tsoffin shugabannin kasashen Afirka uku da suka hada da Jaochim Chissano na Mozambik da Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya da kuma Kgalema Motlanthe na Afirka ta Kudu ake sa rai suka jagoranta. Sai dai Habasha ta karyata yunkurin shiga tsakanin daga shugabannin uku a daidai lokacin rikicin Tigray ke kara tsanani. Abin da ake fargaba a nan shi ne ko da gwamnatin Habasha ta murkushe mayakan to za a samu wasu daga cikinsu da za su shiga yakin sunkuru.

Yakin neman zabe a Yuganda ya kankama 

Yakin neman zabe mai muni a Yuganda wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga a sharhin da ta yi na halin da aka shiga a Yuganda gabanin zaben shugaban kasar. Ta ce a ranar Jumma’a da ta gabata aka sako dan adawa Bobi Wine daga kurkuku, daga nan kuma ya koma yakin neman zabe yana mai cewa ba za su mika wuya ga cin zalin da ‘yan sanda ke musu ba.

Karin Bayani: Bobi Wine ya zame wa Yuganda ala-kakai

Uganda Festnahme Robert Kyagulanyi aka Bobi Wine
Bobi Wine dan adawar kasar YugandaHoto: Abubaker Lubowa/REUTERS

Shi dai Bobi Wine dan shekaru 38, mawaki ne ya rikide ya zama dan siyasa, shi ne babban mai kalubalantar shugaban kasa Yoweri Museveni a zaben da zai gudana cikin watan Janerun 2021. Tun a makon da ya gabata aka ga alamun cewa za a fuskanci tashe-tashen hankula a yakin neman zaben. Hotunan sojoji da fararen hula dauke da makamai sun mamaye kafafan sada zumunta, an kuma kashe mutane da dama. ‘Yan adawa sun dora alhakin tashe-tashen hankulan a kan gwamnati. 

An dakatar da Ahmad Ahmad daga CAF 

Sport Fussball CAF-Präsident Ahmad Ahmad
Ahmad Ahmad shugaban hukumar CAFHoto: picture-alliance/empics/R. Wilkisky

A labarin da ta buga mai taken Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Fifa ta dakatar da shugaban Hukumar Kwalllon Kafar Afirka, CAF, Ahmad Ahmad, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce badakalar cin hanci da rashawa ta girgiza hukumar Fifa. Ta ce Ahmad Ahmad dai babban aminin shugaban Hukumar Fifa ne Gianni Infantino, kuma a ranar Litinin da ta gabata hukumar da’a ta Fifa ta dakatar da Ahmad tsawon shekaru biyar, bisa laifin yin sama da fadi da wasu kudade da cin amanar mukaminsa na shugaban hukumar CAF. Matakin da aka dauka kansa ya kawar da burinsa na sake zabensa a wannan mukami a watan Maris na shekarar 2021. Tun a wasu shekaru ke nan kuma ake zargin Ahmad wanda dan kasar Madagaska ne da cin zarafin mata.