Afirka a jaridun Jamus: 17.04.2020 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.04.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a jaridun Jamus: 17.04.2020

A wannan makon ma annobar Coronavirus ko COVID-19 da ta addabi duniya ta sake daukar hankalin jaridun na Jamus a labaran da suka buga kan nahiyarmu ta Afirka.

Nigeria Abuja Coronavirus Lockdown

Dokar zaman gida saboda Coronavirus

Jaridar Die Tageszeitung ta leka Najeriya ne, inda ta ce al'ummar Najeriya kamar sauran kasashen duniya suna fatan kawo karshen annobar Coronavirus. Ta ce a ranar 30 ga watan Maris aka fara aiki da matakan kulle na tsawon kwanaki 14 a wasu jihohin kasar domin hana yaduwar kwayar cutar Coronavirus. Sai dai bayan daukar matakan, 'yan kasuwa sun tsawwala farashin kaya musamman na abinci, yayin da wasu kayayyakin kamar sabulun wanke hannu da aka fi sani da Hand Sanitizer suka bace a kasuwanni.

Tsawaita dokar zaman gida

Jaridar ta ce ko da yake an dauki matakan ne domin kare al'umma, amma tuni wasu ke fatan kawo karshen matakan cikin gaggawa. Ana kuma cikin haka sai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanar da tsawaita dokar hana fita da makonni biyu, lamarin da ya sanya wasu 'yan kasar aza ayar tambayar yadda za su iya jurewa wannan mawuyacin hali da suke ciki, domin ana samun wasu bata-gari da ke amfani da wannan dama suna aikata ta'asa, abin da kuma ke sanya jama'a cikin fargaba, wato ga fargabar Coronavirus ga kuma ta miyagu.

Fata na gari wannan shi ne taken labarin da jaridar Der Tagesspiegel ta buga kan matakan kariya da kasar Afirka ta Kudu ta dauka, tana mai cewa Afirka ta Kudu ta yi shirin ko-takwana, yanzu yawan masu kamuwa da Coronavirus a kasar na raguwa, sai dai har yanzu hatsarin kamuwa da cutar bai kau ba.

Yawaitar masu Coronavirus

Jaridar ta ce wuraren hada-hada da cunkoson jama'a a Afirka ta Kudun sun kasance wayam saboda matakan dakile yaduwar corona da mahukuntan kasar suka dauka kimanin makonni uku da suka gabata, wanda kuma zai ci gaba nan da wasu makonni biyu masu zuwa. Kasar dai guda ce a sahun gaba a kasashen Afirka da ke da yawan masu cutar ta Coronavirus. Sai dai kuma matakan ba sani ba sabo da jami'an tsaro ke dauka kan masu karya dokokin takaita yawo a kasar, musamman bakar fata wadanda da ma ke cikin halin ni 'yasu, ya wuce gona da iri.

Uganda Johannesburg Coronavirus Maßnahmen Polizei

Jami'an tsaro na cin zarafi

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi shugabannin kasashen Afirka da dama na amfani da matakan yaki da Coronavirus suna muzguna wa al'umma. Ta ce daga Yuganda zuwa Afirka ta Kudu da Najeriya, jami'an tsaro na daukar matakan rashin tausayawa suna cin zarafin wadanda ake zargi da take dokokin yaki da Coronavirus. Jaridar ta ce a wasu kasashen ma yawan wadanda suka rasu a hannun jami'an tsaro da ke kula da bin dokokin yaki da Coronavirus din, ya zarta yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu.

An fake da guzuma....

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke kira da a daina muzgunawar, suna masu cewa shugabannin mulkin kama karya a wasu kasashen Afirka na fakewa da yaki da Coronavirus, suna cin karensu babu babbaka kan talakawa da 'yan adawa. Jaridar ta kara da cewa yawancin al'umma ba kawai radadin matsin tattalin  arziki dangane da matakan yaki da Coronavirus suke ji ba, sun ma fi shan wahala saboda danniyar da suke fuskanta daga wasu gwamnatoci.

Sauti da bidiyo akan labarin