1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Abdullahi Tanko Bala LMJ
October 16, 2020

Fargabar tashin hankali a zaben kasar Guinea da zanga-zangar adawa da rundunar SARS a Najeriya, na daga cikin batutuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus a wanannan makon.

https://p.dw.com/p/3k3fO
Bildkombo Guinea Präsident Alpha Conde (L) ehemaliger Premierminister und Oppositioneller Cellou Dalein Diallo
Shugaba Alpha Conde na Guinea da jagoran adawar kasar Cellou Dalein Diallo Hoto: Carol Valade and Seyllou/AFP/Getty Images

A sharhin da ta rubuta jaridar die Tages Zeitung, ta yi tsokaci ne kan fargabar tashin hankali a zaben shugaban kasa a Guinea. Jaridar ta ce babbar mai gabatar da kara ta kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya, ta nuna matukar damuwa kan zaben. Haka masu sa ido na kasashen Afirka su ma bakinsu ya zo daya, inda suka nuna damuwa kan yiwuwar aukuwar tarzoma da kalaman batanci da kuma kabilanci. Jaridar tace yayin da zaben ke karatowa, haka ma fargabar tashin hankali ke karuwa a tsakanin al'ummar kasar ta yammacin Afirka. Shekaru 20 da suka wuce kasar ta fuskanci yakin basasa sakamakon yaduwar tarzoma daga kasashen Liberia da Saliyo.

Sai dai a wannan karon lamarin ya banbamta. Akwai dai yaduwar masu da'awar jihadi a Mali da Burkina Faso da kuma Nijar. Abin la'akari dai shi ne idan rikici ya fara a Guinea da ke fara zabe a wannan Lahadi, yana iya yaduwa zuwa Ivory Coast wadda ita ma za ta gudanar da zabe a karshen wannan watan na Oktoba da kuma kasashen Ghana da Burkina Faso da Nijar da za su gudanar da nasu zabukan a watan Disamba. A duka wadannan kasashen, shugabannin wadanda farinjininsu ke dusashewa suna fafutukar neman tazarce. An ga halin da aka shiga a Mali wanda ya kai sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da 'yan kasar suka yi ta murna da jinjina ga sojojin da suka yi juyin mulkin.

Kiran kwantar da hankali

Shugaban kasar Alpha Conde mai shekaru 82 a duniya ya tsaya takara domin neman tazarce karo na uku a karagar mulki, bayan wa'adin mulki biyu na shekaru biyar-biyar da ya yi a baya. Jagoran adawa Cellou Dalein Daillo da Shugaba Conde sun yi kira ga magoya bayansu, su tausasa harshe su kuma kai zuciya nesa da tada husuma domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Cartoon SARS - spezielle Polizeigewalt
Sanar da rusa rundunar SARS, ba ta sa an daina zanga-zanga a Najeriya ba

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta ne akan rushe rundunar musamman ta SARS ta 'yan sandan Najeriya. Jaridar ta ce wannan nasara ce ta farko ga dukkan 'yan Najeriya da suka shafe kwanaki suna bayyana bacin ransu a kafafen sada zumunta da maudu'in da suka yi wa taken: #EndSARS. A ranar Lahadin da ta gab ata, gwamnatin Najeriyar ta sanar a shafinta na Twitter cewa, za ta rushe rundunar ta SARS mai yaki da fashi da makami. Sai dai sabanin yaki da fashi da makamin rundunar ta yi kaurin suna wajen cin zarafi da kuma azabtarwa.

Duk da furucin gwamnatin, masu adawa da rundunar ta SARS ba su da cikakkiyar yarda a kanta, saboda a cewarsu wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin ke irin wadannan kalamai na fatar baki ba. Hasali ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam kamar Human Rights Watch da Amnesty International, sun nuna shakku tare da cewa za ma a iya tura irin wadannan jami'an 'yan sanda na rundunar ta SARS zuwa wasu sassa na aikin dan sanda.

Ba gudu ba ja-da-baya

Masu zanga zangar dai muhimman bukatunsu shi ne a sako dukkan mutanen da rundunar SARS ta tsare, a kuma yi adalci wajen hukunta 'yan sandan da suka aikata cin zarafi sannan a biya diyya ga iyalan wadanda aka ganawa ukuba ko aka ci zarafinsu. Kawo yanzu dai babu wata tattaunawa akan hakan, kuma zanga-zangar ta ci gaba da gudana a fadin kasar, duk da kame da kuma harba barkonon tsohuwa a kan masu wannan zanga-zanga.
Likafar wata ta daga a kungiyar ciniki ta duniya. Wannan shi ne taken sharhin jaridar Frankfurter Allgemaeine Zeitung. Jaridar ta ce 'yan takara biyu ke fafatawa domin samun jagorancin kungiyar Ciniki ta Duniya WTO, sai dai ana gani Ngozi Okonjo-Iweala ta fi samun karbuwa. Har yanzu dai kofa a bude take ga wanda zai jagoranci kungiyar Ciniki ta Duniya WTO, nan gaba a birnin Geneva. Jaridar ta ce abin da yake a bayyane shi ne, a karon farko a tarihin kungiyar, mace ce za ta yi jagoranci a wannan karon.

Kombobild | Ngozi Okonjo-Iweala und Yoo Myung-hee
Ngozi Okonjo-Iweala da Yoo Myung-hee na neman shugabancin WTO

A ranar Alhamis mambobin kasashe a kungiyar sun yi tankade da rairaya a tsakanin masu neman mukamin daga 'yan takara biyar zuwa biyu rak. Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya da Yoo Myung-hee daga Koriya ta Kudu, sune suka kai wannan mataki na karshe. Sai dai kuma batun yanke hukunci da ma sanin a kan wacce za ta dare shugabancin kungiyar, sai a karshen wannan watan na Oktoba ko kuma a farkon watan Nuwamba mai zuwa.