1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
April 2, 2021

Yunkurin juyin mulki a Nijar da halin da ake ciki a Mali da Mozambik da kuma wanke Laurent Gbagbo da Kotun Hukunta Masu Aikata Laifukan Yaki ta Duniya ta yi, na daga cikin batutuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/3rWzT
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Sojoji sun murkushe yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a NijarHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung ta rubuta gajeren labari ne game da yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar. Ta ce bayanai a hukumance da jami'ai suka bayar, sun ce an murkushe wani yunkurin juyin mulki bayan harbe-harbe da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Yamai babban birnin kasar da asubahin ranar Laraba. Majiyoyin tsaron kasar sun ce wasu sojoji sun kai hari kan fadar shugaban kasa, amma dakarun da ke tsaron fadar sun mayar da martani suka kuma katse hanzarin sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin. Jaridar ta ruwaito mazauna birnin na cewa, tun da misalin karfe uku na dare suka yi ta jin karar harbe-harbe da manyan bindigogi a wurare da dama na birnin. A wannan Jumma'a, ake bikin mika mulki ga sabon zababben shugaban kasar ta Nijar Bazoum Mohamed da zai maye gurbin Mahamadou Issoufou. Sai dai 'yan adawa da suka sha kaye a zaben na watan Fabrairu sun ki amincewa da nasarar da Bazoum Mohamed ya samu. An dai haramta duk wani gangami na zanga-zanga.
Yanzu kuma sai makwabciyar Nijar din wato kasar Mali, inda har wa yau jaridar ta Die Tageszeitung ta ruwato wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin dakarun kasar Faransa a Mali da karya dokokin kare hakkin dan Adam sakamakon wani harin bam a kan mahalarta bikin aure a kauyen Bounti a ranar uku ga watan Janairun wannan shekara. Harin dai ya halaka mutane 22. Gwamnatin birnin Paris ta mayar da martani cikin fushi, inda ta yi watsi da zargin tana mai cewa jiragen saman yakinta samfurin Mirage sun hango wani taron masu ikirarin jihadi na kungiyar Katiba Serma ne, suka kuma yi musu ruwan bama-bamai. Jaridar ta ce takaddamar da ta barke tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a Malin, ka iya yin babbar illa ga yakin da ake yi da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya dai, ya ce harin haramtacce ne wanda kuma bai dace ba domin kan farar hula aka kai shi.

Mali I Symbolbild I Lage in Diabaly
Zargin sojojin Fransa da kai harin bam kan fararen hula a MaliHoto: Getty Images/AFP/P. Guyot
Niederlande Den Haag I Prozess Elfenbeinküste am Internationalen Gerichtshof
Tshohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo ya fita zargiHoto: Jerry Lampen/AP/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon, ta yi tsokaci kan tabbatar da hukuncin da ya wanke tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da Kotun Hukunta Masu Aikata Laifukan Yaki ta Duniya da ke Birnin The Hague ta yi. Jaridar ta fara ne da tambayar ko Gbagbo zai koma gida ke nan? Jaridar ta ce da yawa daga cikin al'ummar Cote d'Ivoire na dakon komawar tsohon shugaban kasar gida, inda yake da magoya baya da yawa. An zargi Gbagbo da kisa da fyade da cin zarafi da kuma fatattakar abokan adawarsa na siyasa bayan zaben shugaban kasa na 2010. Alkalan kotun sun bayar da umarni a dage dukkan abubuwan da ke kawo tarnakin wajen sakinsa.

A karshe za mu leka kasar Mozambik, inda wasu da ake zargi masu tsananin kishin addini ne suka kai hari a birnin Palma mai tashar jiragen ruwa. A labarin da ta buga kan halin da ake ciki, jaridar Der Taegsspiegel ta ce mutane sun tsere daga birnin sakamakon harin da ya zo mako guda bayan wani hari da aka kai akan wata mahakar gas da ke arewacin kasar ta Mozambik. Jaridar ta ce yanzu haka dai wasu garuruwa a yankin na hannun kungiyar Al-Sunna wa Jama'a mai kaifin kishin addini.