Adesina ne sabon shugaban AfDB | Labarai | DW | 28.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adesina ne sabon shugaban AfDB

Mutane takwas suka nemi kujerar jagorancin bankin na raya kasashen Afirka AfDB kuma bayan kada kuri'a sau shidda suka amince da Adesina.

Tsohon ministan aiyukan gonan Najeriya Akinwumi Adesina ya lashe zaben da aka yi na neman kujerar shugabancin bankin raya kasashen Afirka na ADB. Sakamakon da aka bayyana a hukumance sun nuna cewa Adesina mai shekaru 55 na haihuwa zai gaji Donald Kaberuka na kasar Ruwanda, wanda ya yi wa'adi biyu a wannan mukamin tun daga shekara ta 2005, a daidai lokacin da nahiyar ke fiskantan sauyi a fannoni da dama.

Adesina ya yi nasara ne bayan da aka yi zaben har zagaye shidda, inda ya yi nasarar doke ministocin kudin Cape Verde da Chadi. Masu zaben sun hada da masu hannayen jari a bankin su 80 da shugabanin kasashen Afirka guda 54 da kuma wakilan wasu kasashe 26 da ba na Afirka ba. Mutane 8 ne dai suka yi takarar neman shugabancin wannan banki.