Adawa da matakin Italiya na yakar ta′addanci a Nijar | BATUTUWA | DW | 15.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Adawa da matakin Italiya na yakar ta'addanci a Nijar

Kungiyoyin masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar sun baiyana adawa bisa matakin Italiya na son girke sojoji a kasar don yaki da 'yan ta’adda a kokarin mayar da kasar sansani na sojoji na kasashen ketare ne.

Tun a wannan Larabar hukumomin kolin kasar Italiya suka tabbatar da fatar su ta girke bataliyar sojan kasar a Jamhuriyar Nijar da niyyar kamawa kasar a yakar ayyukan ta'addanci da kuma kakkabe matsalar bakin haure masu kwarara daga kasashen Afirka su bi ta kasar domin tsallakawa zuwa Turai, batun girke sojan na kasar ta Italiya na ci gaba da haifar da cece-kuce a cikin gida da ma bai wa kungiyoyin 'yan fafatuka da ke adawa da shirin a Nijar tayar da jijiyoyin wuya.

A jimlace kasar Italiya za ta ajiye sojojinta kimanin 470 inda rukunin farko na askarawan zai kunshi soja 150 wanda babban aikinsu shi ne, horas da jami'an tsaron Nijar sanin makamar aikin game da matsalolin da kasar ke fuskanta na hare haren 'yan ta'adda tare da saka ido ga kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira. Kungiyoyin irinsu Alternative Espace Citoyens sun caccaki matakin.

A karshen wannan watan ne majalisar dokokin kasar ta Italiya za ta yi wani zama na musamman don jefa kuri'ar amincewa da matakin gwamnatin kasar na tura sojojinta a kasar ta Nijar.Ko a tsakiyar watan da ya gabata Nijar ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar soja da kasar Rasha don samun tallafi wajen yakar ayyukan ta'addanci.

 

Sauti da bidiyo akan labarin