MNA
July 29, 2019Talla
Duk da kalubalen da mata ke fuskanta a wasan kwallon kafa, a wasu lokutan ma har da kyama, da dama daga cikin mata masu wasan kallon kafa sun ce bakin rai bakin fama.
Ana yi wa wannan sana'a ta kwallon kafa kamar abu mai wahala musamman a arewacin Najeriya.
A wasu lokutan ma ana danganta matan da suka zabi sana'ar wasan kwallon kafa da dabi'un da suka danganci rashin kamun kai. Sai dai sun ce ba dukka aka taru aka zama daya ba, hasali ma a cikin kowacce sana'a ana samun bata gari.