1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara da ake zubarwa a Nijar

Zulaiha Abubakar YB
February 4, 2019

Madam Sule Nalado ta dauki gabarar tattara irin wadannan yara guri guda tare da yaran da iyayensu suka gaza daukar nauyin su a birnin Damagaram.

https://p.dw.com/p/3Chi1
Tödliche Kinderarbeit in Nigeria Chemikalien
Hoto: DW/A. Kriesch

A wannan  makon shirin zai yi nazari kan rayuwar irin yaran nan da a kan haifa a jefar a Jamhuriyar Nijar, irin wadannan yara dai a kan wayi gari ne an tsinci jariri kunshe cikin zanin goyo. Mai unguwa ko dagaci ya sa ayi ta cigiya amma shiru a rasa iyayensu, imma dai suna ji sun yi shiru saboda wasu dalilai ko kuma daga wani yankin aka dauko aka jefar. Ganin yadda wannan mummunar al'ada ta fara zama ruwan dare wata mata a Jamhuriyar Nijar mai suna Madam Sule Nalado ta dauki gabarar tattara irin wadannan yara guri guda tare da yaran da iyayensu suka gaza daukar nauyin su a birnin Damagaram, ko  menene ya ja hanlakinta kan wannan hidima? Ta ce tausayi shi ne abin da ya sanya ta dauki wannan aiki, lamarin da ya sanya ta dauki yara sama da arba'in.

Lokuta da yawa bayan an raini irin wadannan yara sun fara kaiwa munzali sai kwatsam wasu su baiyana kansu a matsayin iyayen irin wadannan yara kuma har su bayar da shaidar da za ta tabbatar da hakan. Shin wadanne matakai ake bi kafin amsar jariri ko yaro daga uwa ko uba wadanda suka kasa daukar nauyin su? Madam Nalado ta ce tana bin mataki na shari'a don kada wani abu ya biyo baya.

Yara da ake zubarwa a Nijar

Wani bincike ya nunar da cewar a wasu lokuttan iyaye mata na irin wadannan jariran da a kan jefar na kusa kuma idonsu na kai, sai dai ba su da ikon yin magana saboda barazana ko dai daga iyayensu ko kuma al'umma, wannan cibiya dai tana kula da masu iyayen ma wadanda wani dalili ya sa suka gaza daukar nauyin 'yayan nasu kamar yadda Malama Halima guda ce cikin iyayen da suka kai 'yayansu wannan cibiya ta fada ta kuma baiyana dalilinta da cewa talauci shi ya sa ta kai yaranta.

Don jin cikakkun bayanai a shirin sai a latsa na saurare kamar yadda ake gani a sama.