A ranar 19 ga wannan wata za´a gana tsakanin Olmert da Abba da kuma Rice | Labarai | DW | 07.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A ranar 19 ga wannan wata za´a gana tsakanin Olmert da Abba da kuma Rice

FM Isra´ila Ehud Olmert ya sanar da cewa zai gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice a ranar 19 ga watannan na fabrairu. Rahotanni sun shaidar da cewa za´a gudanar da wannan taron koli na mutum 3 a birnin Kudus. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa a birnin Makkah na kasar Saudiyya tsakanin Abbas da shugabannin kungiyar Hamas da zumar kafa wata gwamnati hadin kan Falasdinawa. FM Falasdinawa Isma´ila Haniya ya ce ya na fatan cewa za´a cimma wata yarjejeniya a taron na Makkah. Sama da mutane 100 aka kashe sakamakon rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin Fatah da Hamas tun a cikin watan desamba.