A Nijar har yanzu na bautar da mutane | Siyasa | DW | 12.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A Nijar har yanzu na bautar da mutane

Jami'an yaki bauta na MDD sun fara aikin binciken kan al'amuran bauta a Nijar, hakan dai ba su daman sanin inda lamarin yaki da bauta ya kwana Nijar

Wakiliyar hukumar yaki da ayyukan bauta ta Majalissar Dinkin Duniya Urmila Bhoola ce ke jagorantar tanwagar da ta soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki 10 a kasar ta Nijar. Makasudin ziyarar dai shi ne ganewa idanunsu inda kasar ta kwana a game da kokowar da ta ke yi a fannin yaki da nau'o'in bautar dan Adam ta fanononi masu yawa, da ake zargin ana yi a kasar ta Niger. Tun bayan da kasar ta sanya hannu akan wata doka da ta tanadi hukunci ga masu aikata wanann danyan aiki a kasar ta Niger a shekara ta 2003.

Kinderarbeit in der Türkei

Wanann dai ita ce ziyara ta farko da wakiliyar sashen kula da yaki da ayyukan bauta na Majalissar Dinkin Duniyar ta kawo a kasar ta Nijar, inda a tsawon kwanaki hudu za ta gana da wakillan gwamnati da na talakkawa da shugabannin kungiyoyin kare hakkin biladama da jami'an diplomasiyya, domin tattaunawa da su girman matsalar ayyukan bauta a Nijar. Kama daga nau'o'insu, dalillan da ke haddasa su, mummunan tasirin da lamarin ke yi ga rayuwar al'umma, dama kalubalen da Nijar ta ke fuskanta wajan aiwatar da dokar haramta ayyukan bauta da ta dauka tun a shekara ta 2003

Sauti da bidiyo akan labarin