A Jihar Kebbi PDP ta ce APC ta muzgunawa masu zabe | Labarai | DW | 10.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A Jihar Kebbi PDP ta ce APC ta muzgunawa masu zabe

Wakilinmu na Sokoto ya ce a Jihar Kebbi 'yan jam'iyyar PDP mai adawa sun bayyana cewar 'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar sun yi barazana ga masu kada kuri'a domin jin tsoro don kin zabin PDP.

Wakilin namu ya ce 'yan jami'iyyar ta APC sun ce 'yan PDP sun muzgunawa mutanen tare da kamasu ana tsarewa da cin zarafinsu. Kana an yin amfani da kudi wajen jirkitar da hankalin al'umma don kada su zabi jam'iyyar PDP a  cewar Sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP Jihar Kebbi Ibrahim Umar.