ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa a Iraqi | Labarai | DW | 03.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa a Iraqi

Manyan jamiyun siyasa a ƙasar Iraqi sun haɗa ƙarfi wuri guda, a ƙoƙarin su na tabbatar da kafuwar gwamnatin hadin kan kasa. Sai dai shugabannin yan sunni sun ce suna kan bakan su sai P/M Irahim jaáfari ya sauka daga mukamin sa. A waje guda kuma hukumomin ƙasar sun sanya dokar takaita zurga-zurga a birnin Bagadaza domin kare aukuwar wata arangama a yayin da musulmi mabiya darikun sunni dana shiá za su fita domin sallar jumaá. Rikicin ƙabilanci dake faruwa a ƙasar Iraqin na ƙara taázzara tun bayan harin da aka kai a makon da ya gabata a wani masallaci na yan shiá da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. A halin da ake ciki gwamnati ta sanya dubban jamián tsaro waɗanda suka haɗa da yan sanda da sojoji domin yin sintiri a manyan titunan birnin Bagadaza da sauran larduna domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.