Ziyarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy Rwanda | Siyasa | DW | 25.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy Rwanda

Wannan ziyarar za ta taimaka wajen kyautata dangantaka da ta yi rauni tsakanin ƙasashen Faransa da Rwanda.

default

Nikolas Sarkozy da Paul Kagame

Wannan ziyarar ita ce ta farko da wani shugaban ƙasar ta Faransa ya kai Rwanda tun bayan kisan ƙare dangi a Rwanda a shekarar 1994, saboda haka ake ganin wannan ziyarar ita ce mafi wuya da Nikolas Sarkozy ya taɓa yi. Tun bayan kisan ƙare dangin da ´yan ƙabilar Hutu masu matsanancin ra´ayi suka yiwa ´yan Tutsi da ´yan Hutu masu sassaucin fiye da dubu 800, dangantaka tsakanin ƙasashen  biyu ta tsami. Rwanda dai na zargin Faransa da taimakawa gwamnatin ´yan Hutu mai tsattsauran ra´a yi ƙarƙashi shugaba Habya-Rimana har izuwa lokacin kisan kiyashin. Da yawa daga cikin ´yan Rwanda ciki har da shugaba Paul Kagame na da ra´ayin cewa Faransa ta ci-gaba da wannan taimako a lokacin kisan ƙare dangin. Kimanin shekaru biyu da suka gabata lokacin da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta taɓarɓare an jiyo shugaba Kagame yana cewa.

"Ina da ƙwararan shaidu dake tabbatar da hannun Faransa dumu-dumu wajen ginawa tare da agazawa tsohuwar gwamnatin Rwanda da sojojin sa kai masu goya mata baya. Kai tsaye Faransa ta taimaka a kisan ƙare dangi da ya auku a Rwanda."

Wani rahoton binciken da gwamnatin Rwanda ta gabatar a wancan lokaci ya tabbatar da wannan zargin. To sai dai ana saka ayar tambaya dangane da sahihancin wannan rahoto da shugaba Kagame ya sa aka yi. Duk da haka dai wasu masana tarihi masu zaman kansu sun zargi Faransa da taka rawa a kisan na ƙare dangi.

Har yanzu kuwa wasu da suka jagoranci wannan ta´asa suna zamansu a cikin Faransa ba da wata tsangwama ba. A lokacin da Kagame da a da yake zama jagoran ´yan tawaye, ya fatattaki ´yan Hutu daga madafun iko, sojojin Faransa sun kafa wani sansanin tudun mun tsira inda daga nan suka yi ta jigilar ´yan Hutu zuwa ƙetare musamman ma gabashin Kong, inda har yau suke tafiyar da wani yaƙin basasa.

Wani abin da ya ƙara dagula al´amura shi ne ƙarar da wani alƙalin Faransa ya shigar yana tuhumar Kagame da kisan ƙare dangi a shekara ta 2006. Hakan ya sa ƙasashen biyu su janye jakadunsu abin da ya gurgunta hulɗar diplomasiya tsakaninsu har zuwa watan Nuwamban bara. Yanzu haka dai shugaba Sarkozy ya ƙuduri aniyar buɗe sabon babin dangantaka da Rwanda. Frank Mwini alƙali ne a Rwanda ya ce tuni ya kamata a ce Faransa ta ɗauki wannan mataki.

"Gwamnatin Faransa ta daɗe ba ta amince da wannan gwamnatin ta Rwanda ba. Wannan ita ce babbar matsalar da ta janyo tsaiko wajen warware batun kisan ƙare dangin a shari´ance."

To sai dai ba a san yadda Sarkozy zai ɓullowa wannan batu mai sarƙaƙƙiya ba. Abin da ke fili dai shi ne Faransa ba za ta nemi gafara daga gwamnatin Rwanda ba inji wani mashawarcin shugaba Sarkozy. To amma duk da haka warware wannan batu zai dogara ga dubarun Sarkozy a diplomasiyance.

Mawallafa: Marc Engelhardt/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi