Ziyarar Shugaba Rohani na Iran a Italiya | Labarai | DW | 25.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Shugaba Rohani na Iran a Italiya

Batun tattalin arziki dai na zamo babban abin da ziyarar za ta fi mayar da hankali a kai inda kamfanonin kasashen Turai da dama ke hankoron kafa cibiyoyinsu a kasar ta Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani na soma wata ziyarar aiki a wannan Litinin a kasar italiya wacce ta ke ziyara ta farko a kasashen Turai.

Batun tattalin arziki dai na zamo babban abin da ziyarar za ta fi mayar da hankali a kai inda kamfanonin kasashen Turan da dama ke hankoron cin moriyar matakin dage wa Iran takunkumi domin samun damar kafa cibiyoyinsu a kasar.

Ziyarar ta Shugaba Rohani za ta kai shi a kasar Faransa wacce tuni kamfanin jiragen samanta na Airbus ya samu kwangilar sayar wa da kasar ta Iran jiragen sama 114 .

Bayan cin abinci da takwaransa na Itakiya Sergio Mattarella, Shugaba Rohani zai kuma gana da Shugaban Gwamnatin kasar wato Matteo Renzi da yammacin wannan Litinin ,sannan ya karkare ziyarar tasa da ganawa da Paparoma Francis a gobe Talata.