Ziyarar Paparoma a Birtaniya
September 16, 2010Talla
A yau ne Shugaban ɗarikar Roman Katholika, Paparoma Benedict na 16 zai fara ziyarar aiki a ƙasar Britaniya. Mai shekaru 83 da haihuwa, Paparoman zai gana da Sarauniya Elizabeth ta biyu a Edinburgh, dake Scotland. Kimanin 'yan Britaniya miliyan biyar ne 'yan darikar ta Roman Katholik, adadin dake zama kashi tara daga cikin 100 na yawan al'ummar Britaniya. A wannan ziyara ta Paparoma Benedict ta kwanaki huɗu, ana saran zai ziyarci Glasgow, London da Birmingham.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu