Ziyarar Obama a Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ziyarar Obama a Afirka

Sharhunan jaridun Jamus na wannan makon sun fi mayar da hankali ne kan ziyarar shugaban Amirka a kasashen Kenya da Habasha

Za fara ne da jaridar dieTageszeitung, inda jaridar ta ce. Kenya sun gano dan su da ya bace. Domin kuwa Obama a matsayin da yake a kasar Kenya, kasancewa nanne kasar mahaifinsa. Kuma bisa siyasa duk wani fitacce in ya lashe zabe, bayan haka yakan tafi gida don a yi masa tarba ta karramawa. Wannan shi ne ke faruwa a wannan juma'ar 24.07.2015 duk da cewar sai bayan shekaru bakwai da lashe zabe Barack Obama yake kai ziyar tasa.

Nairobi babban birnin kasar Kenya ya cika makel bawai ga masu son kallon Obama kawai ba, amma harda tarin jami'an tsaron Amirka. Jaridar ta ce jami'an leken asirin da ma sojoji Amirka ana iya kallonsu kusan ko wane sako a birnin Nairobi, kai hasalima jiragen sojojin Amirka suna shirye a tashoshin jiragen saman Kenya biyu. Wannan tsauraran matakan tsaro da aka dauka sun tilastawa 'yan kasar Kenya da yawa zama a gida. Domin titunan komai a rude yake.An yi wasti da cin zarafin yara, wannan shi ne karin magana da Jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara da shi. Jaridar na magana ne kan sojojin Faransa da aka samu da hannun wajen yin lalata da wasu samarin Jamhuriyar Afirka Tsakiya. Tabargazar lalata da yara da ya shafi sojojin Faransan dai, ya yi sanadiyar murabus din mataiamakin sakatare janar na MDD a bangaren kare hakkin jama'a, da ke kula da Jamuhuriyar Afrika ta Tsakiya. Flavia Pansieri, ya yi murabus bisa abinda yace wai dalilan rashin lafiya. Murabus din jami'in na MDD ya zo a dai-dai lokacin da ake mahawara bisa lalatar da sojojin Faransa suka yi wa yara a Jamuhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Najeriya ta yi nasara a fannin riga kafi. Wannan kuwa shi ne labarin da jaridar Franfurter Algermein ta ruwaito. Jaridar ta ce a wannan Juma'a 24.07.2015 Najeriya ta yi shagalin murnar shekara guda babu labarin bullar cutar shan inna ko Polio. Wato tun a ranar 24 ga watan Julin bara, babu inda aka samu rahoton cutar. Jaridar ta ce idan dai a 'yan kwanaki ko makwanni kungiyar kula da lafiya ta MDD ta tabbatar da nasara da Najeriya ta yi ikirari, to hakan ya nuna kasashe biyu kacal a duniya suka saura da cutar shan inna, wato kasashen Afganistan da Pakistan masu makobtaka da juna, a yanzu sune kadai ke da sauran masu dauke da cutar. Riga kafin cutar shan inna dai ya gamu da cikas musamman a wadannan kasashe da kungiyayoin kishin addini ke adawa da allular ta Polio.