1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kusan shekara daya da soma mamayar Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
February 20, 2023

Amirka da kasashen Turai na fatan ganin Ukraine ta yi nasara a yakin da ta kwashi kusan shekara guda tana gwabzawa da Rasha.

https://p.dw.com/p/4Nkbf
Amirka na fatan nasarar Ukraine kan Rasha
Amirka na fatan nasarar Ukraine kan RashaHoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Shugaban Amirka Joe Biden zai kai ziyarar aikin kasar Poland a gobe talata, inda zai gabatar da jawabi a gabanin zagayowar ranar da Rasha ta kai wa Ukraine hari da nufin mamaye ta. Babban burin da Biden ya sa a gaba shi ne, taimaka wa Ukraine domin ta samu nasara a kan abokiyar gabarta.

Shugaban kasar Poland Andrzej Duda ya sanar da cewa, jawabin da takwaransa na Amirka Joe Biden zai gabatar a yammacin Talata a birnin Warsaw na da mahinmanci ga duniya baki daya. Dama dai sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya yi shagube a taron tsaro da aka yi a Munich na Jamus, inda ya ce, Biden zai yi bayani game da halin da ake ciki a Ukraine tare da ci gaba da goyon baya ga Ukraine domin ta samu nasara a kan Rasha.

Kasar Poland da sauran kasashen gabashin Turai na kungiyar tsaron NATO za su bukaci karin sansanonin sojan Amirka a kasashen, lokacin ganawa da Shugaba Joe Biden na Amirka. Amma babu tabbas kan irin amsar da za a samu daga Amirka. Duk yadda ta kasanec Amirka tana kara karfafa hulda da Poland.