Ziyara Koffi Annan a Jamhuriyar Demokraɗiyar Kongo | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Koffi Annan a Jamhuriyar Demokraɗiyar Kongo

A rangadin da ya fara nahiyar Afrika, tun ranar 13 ga watan da mu ke ciki, yau ne,Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya kai ziyara kwanaki 3, a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.

Bayan ƙasashen Afrika ta kudu, Madagaskar, da Kongo-Brazaville, Annan ya sauka yau,a birnin Kinshassa, inda zai tantana da shugaban ƙasa Lauran Kabila, da mataimakan sa 4, da kuma shugaban tawagar Majalisar Ɗinki Dunia, William Swing .

Mahimman batutuwa da za su maida hankulla a kai, sun haɗa da, bitar halin da ake ciki ,ta fannin zaman lahia, da kuma shirye shiryen zaɓen shugaban ƙasa da za ayi, a watan juni na wanna shekara.

A gobe idan Allah ya kai mu, Anan zai kiri taron manema labarai, a birnin Kinshassa, kamin ya tashi zuwa Kisangani da ke arewa maso gabacin ƙasar, yankin Majalisar Ɗinkin Dunia, ta tare dakarun ta.

A wannan yanki da ke fama da tashe tashen hankulla, Majalisar, na da dakaru fiye da18.000 , wanda ke tallafawa gwamnatin riƙwan ƙwarya, a ayyukan ta, na samar da zaman lahia.

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta buƙaci ƙungiar gamaya turai, ta aika dakaru, domin ƙara ƙarfi ga tawagar ta.

Babban yaunin da ya rataya a kan wannan rudunoni soja, shine tabbattar da, an shirya zaɓen na watan yuni cikin lumana.