Ziyara Jaques Chirac a Masar | Labarai | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Jaques Chirac a Masar

Shugaban ƙasar France, Jaques Chirac, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Masar.

A ganawar da yayi da shugaban ƙasa Osni Mubarack, sun tantana a game da batutuwa daban-daban da su ka jiɓanici al´ammuran diplomatia, da kuma cinikaya tsakanin France da Masar.

A game da rikicin makaman nuklear kasar Iran, shugabanin 2, sun bayyana aniyar su,, ta aiki kafaɗa da kafaɗa, domin samo bakin zaren warware wannan rikici ta hanyar diplomatia, saɓanin niyar Amurika, ta ɗaukar matakan soja a kann Iran.

Sannan, sun yi na´am, da bada taimako ga al´ ummar Palestinu, da ke shirin shiga wani hali na ƙunci , bayan da ƙasashen turai da Amurika, su ka bayyana tsuke bakin aljihun su, ga gwamnatin Hamas.

A sahiyar yau, shugabanin2, sun girka hukumar haɗin gwiwa tsakanin France da Masar, wace za ta kulla da harakokin saye da sayarwa.

Sannan sun buɗa jami´ar France, a ƙasar Masar.