1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

130808 Iran Turkey

Jones, Dorian (DW English)August 14, 2008

Shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinedjad ya kai ziyara aiki a ƙasar Turkiyya

https://p.dw.com/p/ExDj
Tutar IranHoto: picture-alliance/ dpa

Yau ne shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinejad ,ya fara ziyara kwanaki biyu a ƙasar Turkiyya, domin tattanawa da hukumomin ƙasar a game da halin da ake ciki a rikici nukleya.

Ziyara ta shugaba Mahamud Ahmadinedjad na wakana a daidai lokacin da ƙasar Turkiyya, ta shiga faɗi ta shin shiga tsakanin a taƙƙadama da ta haɗa Iran da ƙasashen duniya, a game da rikicin nukleya.

Saidai kamin zuwa nasa, wannan ziyara ta kasance wani abun gardandami a fagen siyasar ƙasar Turkiyya.

Wsau kafofin sadarwa sun ruwaito cewar, dalilan da yasa aka ɗage ganawar Ahmadinidjad da hukumomin, Turkiyya daga Ankara zuwa Istambul ,shine cewar shugaban na Iran, bai buƙatar kai ziyara diplomatia ta wajibi, ga gwarzon da ya girka ƙasar Turkiyya Mustafa Kemal Attaturk.

Sanan Turkiyya masu alaƙa da ƙasashen turai, da Amurika sun yi Allah wadai da wannan ziyara da suke dauka a matsayin wani mataki na farfaganda.

To saidai a cewar jami´an diplomatia ƙasar Turkiyya, ziyara na da babban mahimmanci, ta la´akari da yadda za ta taimakawa, wajen lafawar ƙura  a rikicin dake cigaba da ruruwa tsakanin Iran da ƙasashe dake tattana batun nuklea, da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

Gohkan Cetinsaya, ƙurraren masani ta fannin mu´amila tsakanin Iran da Turkiyya, bugu da ƙari mashawarci a fadar ministan harakokin wajen Turkiyya:A ganina, a game da wannan batu Turkiyya tayi ƙoƙarin da wata ƙasa ba a taɓa yi ba.

Iran ta san da cewar, itama Turkiyya za ta yi asara idan wani yaƙi ya abku tsakanin Iran da Amurika, saboda haka hukumominTurkiyya a zahiri suna buƙatar samun bakin zaren warware wannan rikici.

A makwanin da suka gabata, ministan harakokin wajen ƙasar Turkiyya Ali Babacan ,yayi ta kai gowro ya na kai mari tsakanin Teheran da Washington.

Wannan yunƙurin ta fannin diplomatiya na  daga sabuwar siyasar gwamnatinTurkiyya tun bayan hawan Abdellah Gül a karagar mulki.

A cewar Soli Ozel wani manazarci akan harakokin siyasa dake jami´ar Bilgi ta ƙasar Turkiyya,zai kara tagomashin gwamnati a yankin gabas ta tsakiya:Babu shakka, wannan sabuwar gwamnati na bada la´akari ga yankin gabas ta tsakiya.A halin Turkiyya na taka rawar gani a yunkurin warware rikici tsaknain Israel da Syria, da halin da ake ciki a Irak, sannan da rikicin  Israela da Palestinu.

A ƙasar Irak allal misali, Turkiyya ta tattana so tari da ´yan Sunni su shiga a dama da su bayan zaben gama gari na shekara ta 2005.

sannan a birnin Istambul ana cigaba da tattanawar sirri, tsakanin tawagogin Damascus da naTel Aviv, da zumar warware taƙƙadama tsakanin Syria da Isra´ila.