1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zirga-zirga ta ruwa na bunkasa a Lagos

September 11, 2018

Al'ummar jihar Lagos na mayar da hankali kan sufurin jiragen ruwa a harkokin zirga-zirgar yau da kullum a sakamakon cunkoson ababen hawa kan manyan titunan jihar.

https://p.dw.com/p/34fJB
Nigeria Unsichere Mini-Boote
Hoto: DW/A. Kriesch

Sufurin jiragen ruwa ya sa mazauna Lagos rage sammako don zuwa wurare neman kudi ko kuma sada zumunci. A da ana shafe kusan rabin yini da mota daga Ikeja zuwa Apapa inda ake gudanar da lamuran kasuwanci, amma da jirgin ruwa ya samu a yanzu kasa da awa guda ake bukata don kaiwa wannan kasuwa. Hasali ma zirga-zirga ta ruwa ta fi araha idan aka kwatanta da daukar acaba ko motar haya.

Masu karamin karfi na Lagos sun fi yaba wannan mataki na sufurin ruwa. Amma su ma 'yan kasuwa suka ce zirga-zirga ta jiragen ruwa na sa su kauce wa bata lokaci da asarar kudi.