1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zimbabwe za ta fara biyan diyya ga manoma fararen fata

October 4, 2024

Gwamnatin Zimbabwe za ta fara biyan diyya ga manoma fararen fata da kuma bakake da aka kwace musu gonakinsu a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe na jam'iyyar ZANU PF.

https://p.dw.com/p/4lQQC
Wasu manoma fararen fata da aka tsare a gidajen yarin Zimbabwe bayan sun shaki iskar 'yanci a 2001.
Wasu manoma fararen fata da aka tsare a gidajen yarin Zimbabwe bayan sun shaki iskar 'yanci a 2001. Hoto: AP

Ministan kudi na kasar Mthuli Ncube shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai, ya ce tuni aka sanya Dalar Amurka miliyan 20 a kasafin kudin shekara ta 2024 duk dai a matakin warware takaddamar da ta biyo bayan kwace gonakin manoma a wajen shekara ta 2000, wanda hakan ya gurgurta harkar noma a kasar ta Zimbabwe.

Karin bayani: Manoma farar fata a Zimbabwe sun fara karbar diyya

Tsohon shugaban kasar Mr. Mugabe shi ne ya kwace gonakin daga hannun manoma fararen fata 'yan asalin kasar wadanda suka fito daga tsatson gyauren 'yan mulkin mallaka, wadanda suka karbe gonakin daga wajen bakaken fata tun a wajen karni na 20.

Karin bayani: Kwaskwarima a dokar filayen noman Zimbabwe 

Shugaba Emmerson Mnangagwa wanda ya hau kan karagar mulki bayan saukar Mugabe daga shugabancin kasar sakamakon matsin lamba, yana ci gaba da yaukaka dangantaka da kasashen Turai tare kuma da fadi tashin ganin an yafe wa Zimbabwe dimbin basukan da hukumomin lamuni ke bin ta musamman IMF.

.