Manoma farar fata a Zimbabwe sun fara karbar diyya | Labarai | DW | 08.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Manoma farar fata a Zimbabwe sun fara karbar diyya

Manoma farar fata 206 ne aka biya su diyyar gonakinsu da aka kwace a kasar Zimbabwe,karkashin sabon shirin rabar da filaye da ke shan suka na shugaba Mugabe.

Ministan kula da filaye na Zimbabwe Didymus Mutasa ya sanarda cewa manoma farar fata 206 cikin 4,000 da aka kwace gonakinsu suka maince su karbi wannan diyyar.

Ministan ya yi kira ga sauran manoma da aka tilasatawa barin gonakinsu shekaru 6 da suka shige da su tuntubi maaikatarsa.

Sai dai kungiyoyi dake goyon bayan manoma sun bukace su da kada su karbi wannan diyar saboda a cewarsu,yawan kudin bai kai darajar gonakin nasu da aka kwace ba.

Gwamnatin Mugabe tace ba zata biya adadin darajar gonakin ba,wadda tace biyan cikakken kudaden ya rataya ne akan Burtaniya da tayiwa kasar mulkin mallaka.

Gwamnatin tace turawan mulkin mallak ne suka sace gonakin daga hannun bakaken fata fiye da shekaru 100 da suka shige.

Masu sukar wannan shiri na Mugabe sunce,sauye sauyen da gwamnatinsa ta kawo sunyi sanadiyar harkokin noma sunyi kasa da 40 cikin dari .