Giwa tattake uwa da danta har lahira
January 4, 2022Talla
Rahotanni daga Zimbabwe na cewa wata giwa ta tattake wata mata da jaririnta dan watanni uku har lahiya a kudu maso gabashin kasar, hukumar kula da wuraren shakatawa ta kasar ta ce matar mai shekaru 23 da haihuwa ta gamu da ajalinta ne yayin da take komawa gida bayan da ta je ziyarar gidajen 'yan uwa da abokan arziki a lokacin bikin sabuwar shekarar.
Arangamar giwaye da sauran namun jeji da mutane a wasu yankunan kasar Zimbabwe na zama babbar mataalar da ke addabar mazuan bayan gari, a cewar rahotannin hukumoin kasar akalla mutane 40 namun jeji suka kashe tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2021, matsalar da masana ke danganta shi da yawan karuwar jama'a.