1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe ta amince da tabar Wui-Wui

April 28, 2018

Mahukunta a Zimbabuwe sun amince a hukumance da a fara noma tabar Wui-Wui a kasar saboda amfani na kimiyya musamman wajen hada magunguna.

https://p.dw.com/p/2wqa5
Cannabis Pflanze Marihuana
Hoto: Fotolia/Unclesam

Gwamnatin kasar Zimbabuwe ta amince a hukumance da a fara noma tabar Wui-Wui a kasar, saboda amfani na kimiyya musamman wajen hada magunguna. Daga yanzu a cewar gwamnatin duk wani manomin tabar, na iya zuwa ma'aikatar lafiya don samun lasisin yin hakan, sai dai fa akwai tsauraran matakan hana jama'a wuce makadi da rawa.

Mahukuntan na Zimbabuwe sun ce daya daga cikin sharudan, shi ne tilas ne mutum ya kasance dan kasa ko mai cikakkun takardun zama, yayin da su kuma kamfanoni, sai wadanda suka mallaki cikakkun takardu. Lasisin dai na tsawon shekaru biyar ake bai wa masu sha'awar noma tabar ta Wui-Wui, da kuma kae iya sabonta shi.