1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky zai gana da shugabannin EU

February 3, 2023

Shugaban kasar Ukraine Volodymr Zelensky na shirin ganawa da wasu shugabannin EU ciki har da Ursula von der Leyen a Kyiv kan bukatar kasar domin tattana batun shiga kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/4N3Fc
Shugaban Ukraine Zelensky tare da Shugabar hukumar EU Ursula von der LeyenHoto: Sergei Supinsky/AFP/Getty Images

Shugabar hukumar Turai Ursula von der Leyen da kuma shugaban majalisar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Charles Michel za su gana da shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky a birnin Kyiv. Shugabannin biyu za su tattauna ne kan kokarin da Ukraine din ta ke yi na shiga kungiyar ta EU kamar yadda Shugaba Zelensky ya bukata. Sai dai kuma EU ta ce akwai tarin matakai da za a bi kafin Ukraine ta samu damar zama mamba a kungiyar.

Sai dai ana sa rai shugabannin su tattauna batun takunkuman da EU ta kakkaba wa Rasha yayin da kungiyar ke shirin bayyana sabbin takunkuman da za ta kakaba mata a daidai lokacin da ke dab da cika shekara guda da fara yakin. Sauran batutuwan da za su tattauna sun hada da tallafin kudi da kuma makamai ga Ukraine da ma yunkurin ci gaba da fitar da abinci da kuma tallafin sake gina kasar da kuma shirye-shiryen zaman lafiyarta.