1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen gwamnonin Bauchi da Kaduna

April 29, 2011

Bisa ga dukkan alamu PDP ta kama hanyar sake mulkin jahar Bauchi a karo na huɗu, inda gwamnan jahar Isa Yuguda ya yi wa abokan hamayya fintinkau. Sai dai akwai ƙalubale a gaban jami'an ƙasar da aka zaɓa na cika alƙawura

https://p.dw.com/p/116dg
Tantance masu zaɓe a NajeriyaHoto: dapd

A Tarayyar Najeriya an sanar da sakamakon zaɓukan jihohin Kaduna da Bauchi wanɗanda da aka yi ranar Talatar da ta gabata, sai dai an samu matsaloli na rashin fitar mutane, kana an samu rahotannin satar akwatuna. Misali a jahar Bauchi, matsaloli sun tilastawa hukumar zaɓe ta INEC suke zaɓukan ƙananan hukumomin Ningi da Misau. A jahar ta Bauchi sakamakon farko ya nuna jam'iyyar PDP mai mulkin jaharce ke kan gaba, yayinda sau CPC da ANPP da ACN ke biye mata a baya. Waɗannan jihohin dama an ɗage zaɓensu ne, a sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓe. Kawo yanzu a jahar Kaduna a dai-dailokacin da muke wallafa wannan labarin, ba'a kamma fitar da sakamakon zaɓen ba, inda hukumar zaɓe ke ci gaba da tattara alƙaluma.

Ƙalubalen gwamnonin da aka zaɓa

A Tarayyar Najeriya bayan kammala zaɓukan ƙasa daga matakin jaha izuwa Tarayya, a yanzu abinda ya rage shine ƙalubalen dake gaban shugabannin da aka zaɓa, na cika wa talakawa alƙawuran da suka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, misali na kyautata musu jin daɗin rayuwa. Domin aksarin 'yan siyasa a ƙasar suka yi wa talakawa romon baka, amma da zaran sunci zaɓe, ba sa tinawa da waɗanda suka zaɓe su, balle alƙarin da suka yi.

A ƙasa kuna iya sauron sauti a rahoton wakilinmu Babangida Jibril a Kano da kuma Ado Abdullahi Hazzad daga Bauchi.

Mawallafi: Ahmadu Tijjani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman