Zargin amfani da iska mai guba a Siriya | Labarai | DW | 12.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin amfani da iska mai guba a Siriya

Gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kasar na cigaba da zargin juna dangane da amfani da wata iskar gas mai guba da aka yi a lardin Hama a Juma'ar da ta gabata.

Der syrische Präsident Bashar al-Assad während eines Interviews für AFP

Shugaban Siriya Bashar al-Assad

Gidan talabijin din gwamnatin Siriya ya ce 'yan tawayen kasar da ke da nasaba da kungiyar jihadin nan ta Al-Nusra Front sun yi amfani da iskar mai guba a Juma'a da ta gabata lokacin da suka kai wani farmaki kauyen Kafr Zita, lamarin da ya yi sanadin rasuwar mutane biyu yayin da wasu sama da dari suka galabaita.

Ita kuwa hukumar kare hakkin bani adama ta Siriyan da ke da goyon bayan 'yan adawar kasar ta bakin guda daga cikin jami'anta Rami Abdel Rahman ta ce al'ummar kauyen na Kafr Zita sun fuskanci matsala ta numfashi yayin da wasunsu suka nuna alamu ta shakar guba bayan da sojin gwamnati suka yi luguden wuta a kauyen.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake kokarin raba Siriyan da mamakanta masu guba, bayan da aka fsukanci makamacin wannan yanayin a shekarar da ta gabata inda mutane da dama suka rasu ciki kuwa har da kananan yara.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar