Zanga-zangar ′yan kwadago a Faransa | Labarai | DW | 19.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar 'yan kwadago a Faransa

Adadin masu fita wannan zanga-zanga na ci gaba da samun koma baya tun gangami da aka fita a fadin kasar a ranar 12 ga watan Satimba.

Dubban masu zanga-zanga sun hau titunan Faransa a wannan rana ta Alhamis domin nuna adawa da sauyin da Shugaba Emmanuel Macron ke da shi kan harkokin da suka shafi kwadago a kasar. Sai dai yadda aka samu koma baya na yawan mutane da ke fita wannan zanga-zanga ya ragewa gangamin armashi.

Adadin masu fita wannan zanga-zanga na ci gaba da samun koma baya tun gangami da aka fita a fadin kasar a ranar 12 ga watan Satimba inda sama da mutane 250,000 suka halarta. Francoise Celestine 'yar fansho ce me shekaru 65 da ta fita wannan gangami da babbar kungiyar kwadago ta CGT ta shirya ta yi tsokaci kamar haka:

"Shi shugaba Macron na fitar da doka wacce ya ce domin ni aka yi ta, amma fa ni ina ganin ya yi ne kawai saboda masu kudi, baya duba mu 'yan fansho da ma'aikata."

Kimanin masu zanga-zanga 25,000 ne suka fita gangamin a birnin Paris sabanin 60,000 da suka fita a ranar 12 ga watan na Satimba.