Zanga-zangar neman kafa Biafra a Najeriya | Siyasa | DW | 23.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar neman kafa Biafra a Najeriya

Masu fafutukar ganin an kafa kasar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi gangami ko'ina a duniya domin neman biyan bukata.

To ko da yake wasu sassan sun bi wannan umarni a shiyyar musamman kudu maso gabashin Najeriya ,sai dai bayanai sun nuna cewar da daman kabilar ta Igbo sun yi shakulatan bangaro da wannan umarni inda kuma suka ci gaba da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba.

Masu zanga-zangar na son a saki Nnamdi Kenny Okwu Kanu mai fafutuka

Dama dai mahimman gurare inda aka tsammaci bin wannan umarni dari bisa dari sune biyu Onitsha da ke Jihar Anambra da kuma Aba da ke Jihar Abia a yankin kudu maso gabashin na Najeriya,kuma haka din ne ya faru,domin da daman 'yan goyon bayan 'an rajin na Biafra sun kasance zaman dirshan a gidaddajinsu,inda bayanai suka nunar da daman Ofisoshi na Gwamnati da na kamfuna da kuma kasuwanni sun kasance a rufe,sai dai kuma Jami'an tsaro sun kasance a kusan ko'ina don zaman ko ta kwana.Wannan ranar dai 'yan kabilar ta Igbo da ke rajin kafa kasar ta Biafra daga cikin Najeriya sun dauketa a matsayin ranar zanga-zanga ta lumana da kuma zaman dirshan a gidajensu,domin bayyanawa Duniya muradansu,da suka hada da bukatar gwamnatin Najeriya ta sako Nnamdi Kenny Okwu Kanu mai fafutuka kafa kasar Biafra da gwamnatin Najeriya ke tsare da shi.

Sauti da bidiyo akan labarin