1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga - zangar mayaƙan yankin Neija Delta

July 7, 2010

Wasu mayaƙan yankin Neija Delta sun buƙaci a sallami Ministan kula da yankin

https://p.dw.com/p/ODBM
Hoto: picture alliance / dpa

Kimanin mayaƙan sa kai dubu ɗaya ne daga yankin Neija Delta mai arziƙin man fetur dake Nijeriya suka gudanar da wata zanga - zanga a garin Gwagwalada wanda ke kusa da Abuja - babban birnin Nijeriya, bisa nuna rashin jin daɗin su game da abinda suka ƙira da cewar, yin watsi da su ne a cikin shirin yin afuwar da marigayi shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa 'Yar'adu'a ya ɓullo da shi. Masu jerin gwanon sun buƙaci gwamnatin Nijeriya ta cire ministan dake kula da sha'anin yin afuwar, domin - kamar yadda suka ce basu sami damar yin rajista - a ƙarƙashin shirin ba.

Shrin dai ya tanadi bayar da kuɗi ga duk ɗan tawayen da ya amince da yin watsi da tada hankali a yankin na Neija Delta.

Tun cikin shekara ta 2006 ne mayaƙan sa kai na yankin Neija Delta suka tsaurara hare - haren da suke ƙaddamar wa akan manyan kamfanonin haƙar man fetur na ƙasashen ƙetaren dake yin aiki a yankin amma tashe - tashen hankular sun yi sauƙi tun bayan wani shirin da hukumomi suka ɓullo da shi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umar Aliyu