Zanga-zangar adawa da ′yan Houthi | Labarai | DW | 24.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da 'yan Houthi

Dubban mutane ne suka fantsama kan titunan birnin Sanaa na kasar Yemen don nuna rashin amincewarsu da karbe ikon da 'yan kungiyar Houthi da ke bin tafarkin shi'a suka yi.

Masu zanga-zangar ciki kuwa har da mata da yara kanana sun yi ta rera kalamai na adawa da 'yan Houthi din da kuma kone hotunan shugaban kungiyar Abdulmalek al-Huthi lokacin da suke kewaya sassa daban-daban na birnin na Sanaa.

Masu zanga-zanagar sun kuma isa gidan tsohon shugaban kasar Abdrabuh Mansur Hadi don nuna masa rashin amincewarsu da murabus din da ya ce ya yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kasashen duniya dai sun nuna rashin amicewarsu da karbe ikon da 'yan Houthi din suka yi har ma Kasar Amirka ta ce ta tsaida duk wasu ayyuka da take na taka birki ga mayakan Kungiyar Al-ka'ida a Yemen.